logo

HAUSA

Me taron kolin FOCAC na Beijing zai kawowa Afirka?

2024-09-11 08:02:07 CGTN Hausa

Dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka ta zarce lokaci da sarari, ta haura tsaunuka da tekuna, kuma ta jure zamani. Kafa dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC a shekarar 2000 ya kasance wani muhimmin ci gaba a tarihin dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka.  A cikin shekaru 24 da suka gabata, musamman ma a wannan sabon zamani, kasar Sin ta samu ci gaba hannu da hannu tare da 'yan 'uwanta na Afirka bisa sahihanci, da sakamako na hakika, cike da shauki da imani. Mun tsaya kafada da kafada da juna domin kare hakki da muradunmu a lokutan da duniya ke fuskantar sauye-sauye. Mun kara karfi da juriya tare, ta hanyar dunkulewar tattalin arzikin duniya, da samar da fa'ida ta gaske ga biliyoyin jama’ar Sinawa da Afirka. Mun  fuskanci  bala'u da annoba tare mun kuma yi yaki da su tare, mun samar da labarai masu ratsa jiki na alakar Sin da Afirka. Kullum muna tausayawa juna da kuma tallafa wa juna, mun  kafa misali mai kyau na sabon nau'in dangantakar kasa da kasa. Wadannan kalamai masu ratsa zuciya na daga cikin jawabin shuguban kasar Sin Xi Jinping na bude taron FOCAC na 2024 da aka gudanar a makon jiya wato tsakanin ranakun 4 zuwa 6 ga wannan wata. Wanda ya gudana a karkashin taken “Hada hannu don ciyar da zamanatarwa gaba, da gina al'ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya.  

Mahalarta dandalin da masu lura da al'amuran yau da kullum sun yaba da daukaka alaka a matsayin jagoranci mai hangen nesa, kuma sun gamsu da tsarin da aka tsara, wanda zai iya samar da fa'ida mai yawa ga Afirka, da inganta zamanantar da kai kafada da kafada, da daukaka hadin gwiwar Sin da Afirka zuwa sabon matsayi. Girman dangantakar ya nuna kudurin kasar Sin da himma wajen kara daidaitawa da raya dabarunta na kasa da kasashen Afirka. Inda aka zartas da sanarwar hadin gwiwa kan gina al'ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya daga dukkan fannoni a sabon zamani da kuma shirin aiwatar da shirin na FOCAC na shekaru uku masu zuwa.  Kuma Kasar Sin ta yi alkawarin bayar da tallafin kudi yuan biliyan 360 kwatankwacin dala biliyan 51 don aiwatar ayyukan da ke cikin wannan sanarwa. A cikin shekaru uku masu zuwa, kasar Sin za ta ba da damar horar da 'yan Afirka kusan 60,000 musamman mata da matasa. 

Koyawa matasan Afirka basira da fasaha shi ne babbar hanyar samun dabarun kasuwanci kuma hanyar fita daga rashin aikin yi da talauci.  Matasan Afirka a yau sun zabi kasar Sin wajen samun horo saboda ingantaccen ilimi, da ingancin rayuwa, da samun ilimi bisa tsari mai kama da na gida. Irin wadannan shirye-shiryen musaya sun kuma sa kaimi ga fahimtar juna, abokantaka da cudanyar al'adu a tsakanin jama'ar Sin da Afirka. (Sanusi Chen, Mohammed Yahaya, Saminu Alhassan)