logo

HAUSA

An kaddamar da gasar fasahohin sana’o’i ta duniya karo na 47 a kasar Faransa

2024-09-11 11:17:40 CMG Hausa

An kaddamar da gasar fasahohin sana’o’i ta duniya karo na 47 a birnin Lyon dake kasar Faransa a jiya.

Mutane fiye da 1400 daga kasashe da yankuna kimanin 70 sun hallara a gasar na wannan karo. Sin ta tura mutane 68 don halartar gasar, wadanda za su halarci dukkan wasanni 59 a gasar a fannonin fasahar jigilar kaya, da fasahar gine-gine, da fasahar kere-kere, da fasahar sadarwa, da fasahar zane, da fasahar hidimar zamantakewer al’umma da sauransu. Matsakaicin shekarun masu halartar gasar ya kai 22, kana wannan ne karo na 7 da kasar Sin ta tura tawaga don halartar gasar, inda take da mafi  yawan ‘yan wasa da kuma yawan wasannin da za su halarta a tarihi. (Zainab Zhang)