logo

HAUSA

Sin: Ya kamata a sa kaimi ga kwantar da hankali a kasar Ukraine

2024-09-11 10:01:50 CMG Hausa

A jiya ne, kwamitin sulhun MDD ya gudanar da taro kan yanayin jin kai na kasar Ukraine cikin gaggawa, inda mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Geng Shuang ya bayyana cewa, aikin dake gaban komai a halin yanzu shi ne magance tsananta yakin da bazuwarsa zuwa sauran wurare, kuma bai kamata bangarori daban daban su rura wutar rikici ba, ya kamata a gaggauta sa kaimi ga kwantar da hankali a kasar Ukraine.

Geng Shuang ya yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su yi hakuri, da magance kai hari ga fararen hula, da ababen more rayuwar jama’a, da wuraren ajiyar makamashin nukiliya kamar tashar samar da wutar lantarki ta makamashin nukiliya da sauransu. Ya ce, yaki zai haifar da karin hasarori, ya kamata a tsagaita bude wuta da daidaita matsalar ta hanyar siyasa da ta dace da moriyar bangarori daban daban.

Haka zalika Geng Shuang ya bayyana cewa, Sin ta jaddada ra’ayinta kan batun Ukraine, wato sa kaimi ga yin shawarwari cikin lumana da kuma daidaita matsalar ta hanyar siyasa. Geng Shuang yana fatan kasar Amurka ta ba da taimako a yunkurin tsagaita bude wuta a kasar Ukraine, maimakon takama kan yawan makamai da ta samar wa Ukraine, sa’an nan ta daina shafa kashin kaza kan Sin da sauran kasashe, wadanda ke kokarin wanzar da sulhu. (Zainab Zhang)