Kasar Sin na goyon bayan warware sabanin dake tsakanin kasashen Gabas ta Tsakiya ta hanyar tattaunawa
2024-09-11 20:42:35 CMG Hausa
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya bayyana a yau Laraba cewa, kasarsa na goyon bayan kokarin da kasashen yankin Gabas ta Tsakiya ke yi na warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna, domin cimma zaman makwabtaka cikin aminci mai dorewa.
Li Qiang ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da sakatare janar na kungiyar hadin kan kasashen yankin Gulf (GCC), Jasem Mohammed Albudaiwi.
Ya kuma yi kira ga Sin da kasashen kungiyar GCC su karfafa daidaita dabarunsu na ci gaba da gaggauta tsarin cimma yarjeniyoyin ciniki mara shinge.
Firaministan na Sin ya kuma gana da wakilan kungiyar ’yan kasuwa ta Saudiyya, inda ya bukaci kamfanonin Saudiyyar su kara shiga kasuwar kasar Sin tare da zuba jari da karfin gwiwa. (Fa’iza Mustapha)