logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin na fatan daidaita ci gaba bisa manyan tsare-tsare tare da Saudiyya

2024-09-11 10:27:08 CMG Hausa

Firaminstan kasar Sin Li Qiang ya bayyana a jiya Talata cewa, yana fatan kasashen Sin da Saudiyya za su daidaita ci gabansu bisa manyan tsare-tsare, da daukaka dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa babban matsayi ta hanyar ziyararsa a kasar. 

Li ya isa kasar Saudiyya jiya Talata domin ya jagoranci taro karo na hudu na babban kwamitin hadin gwiwa tsakanin Sin da Saudiyya, da ziyarar aiki a kasar ta Saudiyya bisa gayyatar da yarima mai jiran gado kuma firaministan kasar Saudiyya Mohammed bin Salman Al Saud ya yi masa.

Da yake maganan kan dadadden zumunci dake tsakanin Sin da Saudiyya, Li ya ce, tun bayan kulla huldar diflomasiyya shekaru 34 da suka gabata, ta hanyar hadin gwiwa da bangarorin biyu suka yi, dangantakar Sin da Saudiyya ta samu ci gaba mai armashi, inda ta samar da sakamako mai kyau cikin hadin gwiwa a aikace.

Ya kuma bayyana fatan cewa, ziyarar tasa za ta kara fadada hadin gwiwar moriyar juna a fannoni daban daban, da zurfafa zumuncin dake tsakanin jama'ar kasashen biyu, da kara samun ci gaba a dangantakar dake tsakanin Sin da majalisar hadin gwiwar yankin Gulf ko GCC, da kuma Sin da kasashen Larabawa.

Saudiyya ita ce zangon farko na rangadin kwanaki hudu da yake yi a Gabas ta Tsakiya, wanda daga bisani zai karasa Hadaddiyar Daular Larabawa. (Mohammed Yahaya)