Wakilai 20 daga kasar Tunisiya sun isa Najeriya domin halartar babban taro a kan sha’anin tattalin arziki
2024-09-11 09:27:57 CMG Hausa
Wakilai 20 na ’yan kasuwa daga kasar Tunisiya sun isa Najeriya domin halartar taro kan sha’anin tattalin arziki tsakanin Najeriya da Tunisiya, inda yayin taron za a bullo da sabbin damarmakin zuba jari a tsakanin kasashen biyu.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Ayarin ’yan kasuwar na karkashin jagorancin shugaban majalissar kasuwanci na kasar Tunisiya Mr Anis Jaziri, kuma jakadan Tunisiya a Najeriya Mr Mohsen Antit shi ne ya tarbe su a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake birnin Abuja da yammacin jiya Talata 10 ga wata.
Za dai a shafe mako guda ana gudanar da wannan taron wanda aka fara tun a jiya.
Taron wanda aka shirya shi bisa hadin gwiwa da ma’aikatar harkokin kasashen ketare na Najeriya da kuma takwarar ta masana’antu da harkokin zuba jari. Ana sa ran cewa zai bunkasa alakar hada-hadar kasuwanci a tsakanin Najeriya da kasar Tunusiya.
A lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan da saukarsu, jagoran ayarin Anis Jaziri ya ce, wannan shi ne karo na farko a tarihin da irin wannan tawagar ’yan kasuwa daga Tunusiya suka zo Najeriya hususan domin gudanar da irin wannan taro.
Ya ce, yayin taron za a tattauna a kan bangarori da dama da suka hada da sha’anin gine-gine, fasahar sadarwa, harkokin kiwon lafiya, samar da makamashi mai tsafta da samar da magunguna da kuma wasu bangarorin ci gaban tattalin arziki. (Garba Abdullahi Bagwai)