logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Borno ta sanar da rufe dukkan makarantun jihar sakamakon barazanar ambaliyar ruwa

2024-09-10 10:05:36 CMG Hausa

Gwamnan jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantu kama daga na firamare har zuwa na sakandire a dukkan fadin jihar domin kaucewa asarar rayuka sakamakon barazanar ambaliyar ruwa.

Kwamashinan ilimin kimiya da kirkire-kirkire na jihar Injiniya Lawan Wakilbe ne ya tabbatar da hakan jiya Litinin 9 ga wata a birnin Maiduguri lokacin da yake zantawa da manema labarai. Ya ce, yanzu haka babu karamar hukumar da ba ta cikin barazanar ambaliyar ruwa a jihar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Injiniya Lawan Wakilbe ya ce, an bayar da umarnin rufe dukkannin makarantun ne na tsawon kwanaki 14 har sai an samu saukin ambaliyar ruwan.

Ya ce, gwamnatin ta dauki wannan mataki ne bayan ta tattauna da kwamitin takaita asarar da ka iya faruwa sakamakon ambaliyar ruwa wanda gwamnatin jihar ta kafa, domin dai tabbatar da ganin an ceci rayukan jama’a.

Kwamishinan ya ce, al’umomin da dama ne suka gamu da matsalolin ambaliyar ruwan a bana.

An dai kiyasta cewa, adadin magidanta 23,868 ne da suka fito daga kananan hukumomi 12 dake jihar Borno suka gamu da annobar ambaliyar ruwa a bana musamman a yankin birnin Maiduguri da kananan hukumomin Jere, da Bama, da Biu, da Bayo da Abadama.

Haka kuma ambaliyar ruwan ya yi sanadin rushewar gidaje dubu 2, sannan kuma ya cinye gonaki masu yawan gaske.

An dai danganta ambaliyar ruwa na bana a jihar Borno bisa yawan ruwan sama da aka samu wanda ya sanya madatsun ruwan Alao da na Gadabul suka tunbatsa har aka kai ga bude su. (Garba Abdullahi Bagwai)