Kasar Sin za ta ci gaba da yin aiki tare da kasashen duniya wajen sa kaimi ga raya sha’anin mutane masu bukata ta musamman
2024-09-10 21:26:30 CMG Hausa
Kwanan nan ne aka rufe wasannin Olympics na masu bukata ta musamman na lokacin zafi karo na 17, kuma tawagar wasannin kasar Sin ta zo na daya a jerin lambobin yabo na zinare da mafi yawan lambobin yabo a cikin wasannin shida a jere. Da take mayar da martani kan wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru na yau 10 ga wata cewa, kyakkyawar nasarar da tawagar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ta samu, sakamakon jajircewar da 'yan wasan suka yi ne, kuma hakan ya nuna karara irin ci gaban da aka samu a fannin ‘yan wasa masu bukata ta musamman, da ci gaba da kyautata yanayin rayuwarsu a kasar Sin. Kasar Sin za ta ci gaba da yin aiki tare da kasashen duniya don sa kaimi ga raya sha’anin mutane masu bukata ta musamman a duniya. (Yahaya)