Mataimakin shugaban Ghana ya gabatar da takardun nuna bukatar yin takarar shugaban kasa
2024-09-10 10:06:33 CMG Hausa
Mataimakin shugaban kasar Ghana Mahamudu Bawumia, ya gabatar da takardun nuna bukatar yin takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyarsa ta NPP ga hukumar zaben kasar EC, jiya Litinin a birnin Accra fadar mulkin kasar.
Bawumia, wanda ya samu rakiyar wanda zai masa mataimaki a takarar babban zaben kasar ta Ghana dake tafe a watan Disamban karshen shekara, kuma babban sakataren jam’iyyar NPP Matthew Opoku Prempeh, da sauran kusoshin jam’iyyar, sun bukaci hukumar EC ta yi duk mai yiwuwa wajen gudanar da zabe mai tsafta.
Bawumia, ya ce yana da karfin gwiwar cewa hukumar ta EC za ta cimma nasarar gudanar da karbabben zabe, ba tare da wasu matsaloli ba. Bawumia ne dai mutum na farko da ya gabatar da bukatar takarar shugabancin kasar ta Ghana a zaben karshen shekarar nan ta 2024.
Rahotanni na cewa, da yammacin jiyan, ta hannun shugabannin jam’iyyarsa ta NDC, shi ma tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama, ya gabatar da na sa takardun nuna bukatar yin takarar shugaban kasar. (Saminu Alhassan)