Xi Jinping Ya Taya Murnar Ranar Malamai Ta Kasar Sin
2024-09-10 10:58:38 CGTN Hausa
An kira babban taron ba da ilmi daga ran 9 zuwa 10 a nan birnin Beijing. Babban sakataren kwamitin tsakiyar JKS, kana shugaban kasar Sin, sannan shugaban kwamitin kolin sojan kasar Xi Jinping, ya halarci taron tare da ba da jawabi.
Ran 10 ga watan nan, ita ce ranar malamai ta kasar Sin karo na 40, kuma a madadin kwamitin kolin JKS, Xi ya isar da gaisuwa ga malamai da masu aikin ba da ilmi.
Shugaba Xi ya jaddada cewa, mutunta malamai nagartacciyar al’ada ce ta al’ummar Sinawa tun a lokacin da, kuma ya kamata a daga matsayin malamai a fannin siyasa da kuma cikin al’umma. Kana a daga matsayin sana’arsu, da kuma kara tabbatar da hakkokinsu, da kara kudin shigar malaman makarantar firamare da na midil, har ma da tabbatar da manufar ba da tallafin kudi ga malaman dake aiki a kauyuka, da kuma sa kaimi ga yin kwaskwarima kan tsarin kudin shigar malamai.
Shugaba Xi ya kara da cewa, kamata ya yi, a kare mutunci da hakkin malamai, da rage nauyin dake wuyansu na ayyukan da ba na koyarwa ba, da ma ba da tabbaci ga zaman rayuwarsu bayan ritaya. Kazalika, dole ne a kara ba da lambobin yabo ga fitattun malamai da yayata labaransu, ta yadda za a daga sunansu da mutuncinsu a cikin al’umma. Haka kuma, aikin malamta ya zama daya daga cikin ayyuka mafi samun karubwa a wajen al’umma. (Amina Xu)