logo

HAUSA

Mohammed Idris: Sin ta dade tana mai da hankali kan ci gaban kasashen Afirka

2024-09-10 15:56:11 CMG Hausa

An gudanar da taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka na 2024 a birnin Beijing daga ranar 4 zuwa ranar 6 ga watan Satumba, inda shugabanni daga kasashen Afirka fiye da 50 suka hadu a birnin Beijing. Yayin taron, bangarorin Sin da Afirka sun sada zumunta tsakanin juna, da gudanar da shawarwari kan karfafa hadin-gwiwa, da kuma tsara makoma mai kyau tare bisa jigon “inganta zamanintarwa tare, da gina al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya mai babban matsayi tare”.

Yayin taron, Mohammed Idris, ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na Najeriya, wanda ya zo kasar Sin don halartar taron, ya karbi wata tattaunawa ta musamman da wakiliyarmu Faeza Mohammed Mustapha, inda ya bayyana ra'ayinsa game da dangantakar Sin da Najeriya da sauran fannoni, ga yadda tattaunawar ta kasance: