Wakilin Sin: Bai kamata a yi amfani da ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD wajen tsoma baki cikin harkokin gida ba
2024-09-10 10:21:50 CMG Hausa
Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya ce bai kamata a yi amfani da ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD, wajen tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashen da abin ya shafa ba.
Fu Cong, ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, yayin zaman kwamitin tsaron MDD da ya gudana game da batun ayyukan wanzar da zaman lafiya. Ya ce a halin yanzu, yanayin tsaron kasa da kasa, da na shiyyoyi na fuskantar sabbin sauye sauye. Don haka ya dace a aiwatar da ka’idoji 3 na dogon lokaci na inganta ayyuka, wadanda suka hada da neman amincewar wuraren da za a gudanar da ayyukan, da rashin nuna son kai ko amfani da karfi fiye da bukatar kare kai, da kare manufar ayyukan.
Ya ce mafi yawan kalubalolin dake addabar ayyukan wanzar da zaman lafiya a halin yanzu na da alaka ne da kaucewa ka’idoji, da manufofin ayyukan.
Daga nan sai ya ba da shawarar karfafa hadin gwiwa tsakanin ayyukan wanzar da zaman lafiya da kasashen da ake gudanar da su, kana shugabannin ayyukan su rika nuna dattaku, da tabbatar da da’a, da sanin ya kamata tsakanin dukkanin ma’aikata, da ma daukacin tsarin ayyukan MDD na kyautata samar da daukin gaggawa, don rage tasirin asarar rayuka yayin aukuwar tashe tashen hankula. (Saminu Alhassan)