logo

HAUSA

Jamhuriyar Niger ta kaddamar da shirin rage hayayyafar sauro

2024-09-10 10:49:43 CMG Hausa

Niamey, babban birnin Jamhuriyar Niger, ya kaddamar da aikin dakile sauro tun daga jiya Litinin da misalin karfe 7 na yamma agogon kasar, da nufin rage hayayyafar sauro, wanda shi ne musabbabin cutar zazzabin malaria.

Hukumomin birnin ne suka bayyana haka cikin wata sanarwa, inda suka kara da cewa, cutar na rayuwa ne a wurare mara tsafta da wadanda ke da ruwan da ba ya gudu.

Domin dakile wannan barazana, birnin ya yi kira ga mazauna da su dauki matakan kandagarki, ciki har da kare kayayyaki abinci da abubuwan sha, yayin da jami’ai ke gudanar da aikin.

A cewar jami’an, abu ne mai muhimmanci a lura cewa, ana samun cutar malaria a kasar a duk shekara a yankunan karkara da birane. Haka kuma cutar ce ke kan gaba wajen haifar da rashin lafiya da mace-mace a kasar, musammam tsakanin yara ’yan kasa da shekaru 5 da mata masu juna biyu.

Minisatan lafiya na kasar Garba Hakimi, ya bayyana a ranar yaki da cutar Malaria ta duniya cewa, a shekarar 2022, kasar ta samu mutane miliyan 5.3 da suka kamu da cutar Malaria, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 5,678 daga cikinsu. (Fa’iza Mustapha)