logo

HAUSA

Kasar Sin za ta hada hannu da kasashe mambobin FOCAC wajen aiwatar da sakamakon taron dandalin domin al’ummomin bangarorin biyu su amfana

2024-09-09 20:41:09 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, yayin da ake wata gaba na sabon mafari a tarihi, kasar Sin za ta hada hannu da kasashen Afrika, mambobin dandanlin tattauna hadin kan Sin da Afrika (FOCAC), wajen aiwatar da sakamakon da aka cimma yayin taron dandalin, domin al’ummomin bangarorin biyu su kara amfana.

A makon da ya gabata ne aka yi nasarar gudanar da taron dandalin na FOCAC.

Kakakin ma’aikatar Mao Ning ce ta bayyana haka, tana cewa, a ‘yan kwanakin da suka gabata, shugaban kasar Sin ya sanar yayin taron FOCAC cewa, kasarsa za ta aiwatar da “matakin taimakawa nahiyar Afrika kawar da barazanar nakiyoyi”.

A cewar Mao Ning, a shirye kasar Sin take ta karfafa hadin gwiwa kan harkokin kawar da nakiyoyi da kasashen Afrika, ta hanyar taimakon kayayyaki da bayar da horo da bayar da jagoranci yayin da ake gudanar da aikin da sauran hanyoyi, domin taimakawa nahiyar kawar da hadarin dake tattare da nakiyoyi nan bada jimawa ba, ta yadda za’a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare da samun ci gaba mai dorewa. (Fa’iza Mustapha)