Sin ta gabatar da tsarin aiki bayan ta karbi shugabancin karba-karba na SCO
2024-09-09 11:53:50 CGTN Hausa
Yau Litinin, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta kira wani taron manema labarai, inda ta yi bayani game da karbar shugabancin karba-karba na kungiyar hadin kai ta Shanghai wato SCO da Sin ta yi.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Sun Weidong ya bayyana cewa, Sin ta karbi shugancin taron nan da nan, bayan da aka kammala taron kolin SCO da aka gudanar a Astana a watan Yulin bana, kuma za ta shirya taro karo na 25 na kwamitin shugabannin SCO a nan kasar Sin a badi. Sin za ta yi amfani da wannan zarafi mai kyau wajen kara hadin gwiwarta da kasashen SCO don cika alkwarinsu, da sauke nauyin dake wuyansu, da ma tabbatar da shawarar raya duniya baki daya, da ta tabbatar da tsaron duniya, da ma ta tabbatar da cudanyar al’adu a duniya, matakan da za su taka muhimminyar rawa wajen kiyaye zaman lafiya da wadata mai dorewa a duniya.
Jami’in kasar Sin ya kara da cewa, taron kolin da za a gudanar a badi wani muhimmin sashi ne karkashin tsarin SCO, kuma aiki ne da Sin ta dauka da muhimmanci matuka a wa’adin aikinta. Sin tana sa ran gabatar da wannan biki na hadin gwiwa da samun ci gaba mai armashi, da tabbatar da ganin bangarori daban-daban da su kai ga cimma matsaya daya, da tsai da shirin neman bunkasuwa ciki hadin kai. Ban da wannan kuma, an ce, Sin za ta karbi bakuncin taruka da bukukuwa fiye da 100 a bangaren siyasa da tsaro da raya harkokin tattalin arziki da al’adu duk a karkashin tsarin SCO. (Amina Xu)