logo

HAUSA

Majalisar gudanarwa ta Sin ta taya tawagar ‘yan wasa masu bukata ta musamman murna

2024-09-09 11:43:11 CGTN Hausa

 

Kwanan baya, majalisar gudanarwa ta Sin ta taya tawagar ‘yan wasa masu bukata ta musamman da ta halarci gasar Olympics ta masu bukata ta musamman karo na 17 murna ta wani sako na musamman.

Cikin sakon, majalisar ta ce, a gun wannan gasar, ‘yan wasan masu bukata ta musamman na kasar Sin sun yi iyakacin kokari a gasannin da suka halarta, da kuma bayyana kwarewarsu da ruhin Olympics kwarai, inda suka samu labobin yabo na zinrari 94, da na azurfa 76, da kuma na tagulla 50, abin da ya bayyana cewa, sun tabbatar da ruhin Olympics tare da samun sakamako mai gamsarwa a gasar. Saboda haka hukumomin kasar Sin da al’ummar kasar na alfahari game da nasarar da aka cimma. Kana a nasu bangare, kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin mai rike da ragamar mulki a kasar, da majalisar gudanarwar kasar sun nuna wa ‘yan wasan gaisuwa da fatan alheri.

An ce, tun daga shekarar 2004 wato lokacin da aka gudanar da gasar Olympics ta Athens, tawagar ‘yan wasa masu bukatar musamman na kasar Sin ta kare matsayin farko a fannin yawan lambobin yabo da aka samu a gasannin Olympics na ‘yan wasa masu bukata ta musamman cikin gasannin Olympics 6 a jere. (Amina Xu)