Kafafan yada labarai na Jamus: Ayyukan makamashi mara gurbata muhalli na kasar Sin zai bunkasa ci gaba a Afirka
2024-09-09 10:12:42 CMG Hausa
Bisa labarin da Deutsche Welle na kasar Jamus ya bayar, an ce, ayyukan samar da makamashi mai tsafta na kara yin tasiri a dangantakar tattalin arzikin Sin da Afirka, yayin da cinikayya tsakanin bangarorin biyu ke samun ci gaba cikin shekaru 20 da suka gabata.
A taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC na shekarar 2024 da aka kammala kwanan nan, kasar Sin ta bayyana shirin aiwatar da ayyukan samar da makamashi mai tsafta 30 a Afirka, domin tallafawa ci gaban nahiyar. Bugu da kari, kasar Sin za ta ba da karin tallafin kudi yuan biliyan 360 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 50.8 ga kasashen Afirka cikin shekaru uku masu zuwa.
Rahoton mai taken "Kasar Sin ta kuduri aniyar karfafa huldar makamashi mai tsafta da Afirka." Ya bayyana cewa, Ana sa ran wadannan tsare-tsare za su samar da a kalla sabbin guraben aikin yi miliyan 1. Rahoton ya kara da cewa, tun farkon karnin da muke ciki, cinikayya tsakanin Sin da Afirka ya karu da kashi 17.2 cikin dari a duk shekara. Yayin da a cikin watanni bakwai na farkon shekarar 2024, yawan cinikin ya kai yuan triliyan 1.19 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 168.
Rahoton ya kuma rawaito Christian-Geraud Neema, wani mai bincike na kasar Sin daga Mauritius, wanda ya yi karatu tare da yin aiki a kasar Sin tsawon shekaru goma na cewa, batun makamashi mai tsafta ya kasance kan gaba cikin muhimman batutuwan hadin gwiwar Sin da Afirka a nan gaba. Kana Afirka za ta taka muhimmiyar rawa a tsarin samar da kayayyaki masu amfani sabbin makamashi na kasar Sin, yayin da bukatar nahiyar ta sauyi zuwa yin amfani da makamashi mara gurbata muhalli za ta yi tasiri sosai kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Mohammed Yahaya)