Mataimakin firaministan Sin ya karfafa gwiwar kamfanonin waje da su shiga aikin Sin na neman samun bunkasuwa mai inganci
2024-09-09 10:47:55 CMG Hausa
Mataimakin firaminstan kasar Sin He Lifeng a jiya Lahadi, ya karfafa wa kamfanonin kasashen waje gwiwar shiga cikin harkokin ci gaban kasar Sin mai inganci, da kuma neman karin damammakin kasuwanci a kokarin zamanintar da kasar Sin.
He, wanda kuma mamban ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin bude baje kolin zuba jari da cinikayya na kasa da kasa na kasar Sin ko CIFIT karo na 24, a birnin Xiamen na lardin Fujian dake gabashin kasar Sin.
Mataimakin firaministan ya ce, a matsayin wani muhimmin dandali na inganta hadin gwiwa a bayyane ta hanyar zuba jari a kasashen waje, baje kolin na CIFIT ya zama dandalin kasa da kasa kuma na musamman, inda ya kara da cewa, ci gaban CIFIT na nuni da yadda kasar Sin ke ci gaba da bude kofa ga kasashen waje.
Ya kara da cewa, don kara bude wani sabon babi na zamanintar da kasar Sin, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan muhimman manufofin kasa na bude kofa ga kasashen waje, da inganta karfinta ta bude kofa da fadada hadin gwiwar kasa da kasa, da gina sabon tsarin budaddiyar tattalin arziki a mataki mafi girma. (Mohammed Yahaya)