logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin zai halarci taron kwamitin hadin gwiwa na manyan jami’an Sin da Saudiyya

2024-09-09 19:55:41 CMG Hausa

Daga ranar 10 zuwa ta 13 ga wata, firaministan kasar Sin Li Qiang, zai kai ziyarar aiki kasar Saudiyya, tare da jagorantar taro karo na hudu na kwamitin hadin gwiwa na manyan jami’an Sin da Saudiyya. Haka kuma zai kai ziyara Hadaddiyar Daular Larabawa.

Wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ta fitar yau Litinin, ta ruwaito cewa, Li Qiang zai ziyarci kasashen ne bisa gayyatarsa da yariman Saudiyya kuma firaministan kasar Mohammed bin Salman da kuma mataimakin shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa kuma firaministan kasar, Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum suka yi masa. (Fa’iza Mustapha)