logo

HAUSA

Wang Yi zai halarci taron tsaro na kasashen BRICS a St. Petersburg

2024-09-09 19:59:19 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, zai halarci taro na 14 na manyan jami’an kasashen BRICS dake da alhakin kula da harkokin tsaro da kuma masu bayar da shawara kan batun tsaro, wanda za a yi daga ranar 11 zuwa 12 ga wata, a birnin St. Petersburg na kasar Rasha.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ce ta sanar da hakan a yau Litinin. (Fa’iza Mustapha)