logo

HAUSA

Shugaban Zimbabwe: Zimbabwe da Sin na da matsaya daya a gaban kalubaloli

2024-09-09 14:55:03 CGTN Hausa

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Dambudzo Mnangagwa ya shedawa manema labarai na CMG a kwanan baya cewa, Zimbabwe na fatan karfafa huldarta da Sin, da ma marawa juna baya cikin harkokin shiyya-shiyya da na kasa da kasa, saboda suna da matsaya daya wajen fuskantar kalubaloli.

Mnangagwa ya ce, Sin kawar Zimbabwe ce mai dankon zumunci, kuma sahihiyar abokiya mai amincewa da Zimbabwe, yayin da take kokarin karkata hanyarta zuwa ga samun bunkasuwa. Ya kara da cewa, bunkasuwar yawancin kasashen Afrika na da alaka da ci gaban hadin gwiwarsu da kasar Sin.

Yayin da ya bayyana ra’ayinsa game da takwaransa na Sin Xi Jinping, ya ce, Xi wani shugaba ne mai wayewar kai dake da tunani mai zurfi, ko da yake yana rayuwa a wannan karni na 21, amma tunaninsa na da hangen nesa matuka, zai bullo da makoma mai haske ta nan gaba. (Amina Xu)