Xi ya mika sakon taya murnar cika shekaru 76 da kafuwar kasa ga takwaransa na Koriya ta Arewa
2024-09-09 10:15:40 CMG Hausa
Yau Litinin, babban sakataren kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar, Xi Jinping ya buga wa takwaransa na kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un waya, domin taya kasar murnar cika shekaru 76 da kafuwa.
Xi Jinping ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, gami da yin hangen nesa. Yana fatan karfafa mu’amalar dake tsakanin kasashen biyu kan manyan tsare-tsare, tare da inganta hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Koriya ta Arewa, ta yadda za a kiyaye da inganta da kuma raya dangantakar hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata. (Mai Fassara: Maryam Yang)