logo

HAUSA

Kwallon kafa ya samar wa yara mata dake karkarar kasar Sin sabuwar dama a rayuwarsu

2024-09-09 20:08:08 CMG Hausa


Makarantar firamaren Zhangpan na da mazauni ne a kauyen Zhangpan. Akwai wata siririyar kofa da za ta kai ka harabar makarantar. Song Haibo, shugaban makarantar ya ce, “filin wasan kwallon kafa cikar burinmu ne”. Kafin shekarar 2015, filin wasa daya makarantar ke amfani da shi tare da makarantar sakandare ta Zhangpan.

Liang Yaowu, shi ne malamin dake koyar da wasannin motsa jiki a makarantar firamaren. Ya ce, “galibin ‘yan matan kauyen na da basirar wasanni”. A shekarun 1980, lokacin da Liang ke koyarwa a makarantar sakandare ta Zhangpan, wasu daga cikin dalibansa sun samu sakamako mai kyau yayin da ake gasar wasannin motsa jiki tsakanin daliban lardin. Sakamakon nasarar da suka samu, wasu daga cikinsu, sun samu guraben karatu a makarantun horar da wasanni na matakan birni ko lardi.

A watan Yulin 2015, sassa 6 na gwamnatin kasar Sin suka fitar da wasu ka’idojin gaggauta raya harkokin kwallon kafa a makarantu. Liang ya gabatarwa makarantar shawarar shirya horon kwallon kafa tsakanin dalibai, musamman dalibai mata, wadda ta samu yarda daga wajen shugaban makarantar Song Haibao. Amma Song da Liang dukkansu ba su da ilimin kwallon kafa sosai, don haka, sai da suka fara koyo tun daga matakin farko. Su kan jagoranci daliban wajen atisaye yayin da su kuma ke koyon ilimin kwallon kafa ta hanyar kallon shirye-shiryen bidiyo domin fahimtar ka’idojin wasan.

A 2016, kungiyar kwallon kafa ta mata ta makarantar ta fafata a gasar da aka yi a matakin gunduma, inda ta zo na biyu. Song Haibo ya bayyana cewa, “ ‘yan wasanmu suna da karfin jiki, amma ba su da kwarewa. Mun gano cewa, sai mun dauko kwararru domin su horar da su.” Song ya nemi Li Lei, wani tsohon dan wasan na tawagar dalibai ta kasa, kuma wanda ya kafa kungiyar kwallon kafa ta matasa a birnin Luoyang, domin ya horar da daliban. A watan Mayun 2017, aka kafa ofishin kula da harkokin wasan kwallon kafa na makarantar. Song ne shugaban ofishin, yayin da Liang da Li suka zama masu bayar da horo. Zhang Canbo kuma, wanda shi ne daraktan dake kula da harkokin gudanarwa na makarantar, shi ne mai kula da aikin ba da guzuri.

Tun daga sannan, kungiyar ‘yan wasan take atisayen sa’o’i 2 a kullum bayan an tashi daga makaranta. Li Lei ya furta cewa, “yanayin horon na da wahala. ‘Yan wasan ba su da rigar kungiya, kuma suna karbar horo ne kan siminti. Amma ba su taba korafi ba”. 

Kungiyar na da ‘yan wasa 12 kawai kafin lokacin hutu na lokacin zafi a 2017. Song da masu bayar da horo sun sha wahalar tabbatar da kasancewar ‘yan wasa a kungiyar. Liang Yaowu ya ce, “galibin iyaye sun yi ammana cewa, karatun makaranta shi ne mafi muhimmanci ga ‘ya’yansu. Ba laifi ba ne idan ba su son ‘ya’yansu su fi mayar da hankali kan kwallon kafa”.

Domin rarrashin iyaye su bar ‘ya’yansu su buga kwallon kafa, Song ya shirya taruka 3 da iyayensu. Song ya ce, “mun fahimci cewa daliban da suke karbar horon kwallon kafa sun fi kwazo a makaranta, kuma sun fi wayewa. Wadanda suke da basirar kwallon kafa, za su iya neman kwarewa ta musamman yayin da suke neman gurbin karatun gaba da sakandare”. Ya kara da cewa, kwallon kafa zai iya kara wayar da kan daliban idan suka halarci gasanni a wasu wurare, kuma ya yi alkawarin cewa, makarantar za ta tsara yadda malamai za su taimakawa daliban da karatu a karshen mako.

Liang Mengyan, wadda take aji na 4 a lokacin, tana kaunar wasan kwallon kafa. Bayan ta shiga kungiyar makarantar, ta kara kwazo a makaranta. Don haka, mahaifiyarta wadda da kyar ta bari ta shiga kungiyar, ta kyale ta ta ci gaba da buga kwallon kafa. A watan Oktoban 2017, kungiyar ta fafata a gasar kwallon kafa ta matakin gunduma. Duk da cewa shi ne karon farko da kungiyar ta shiga gasa, duk da kuma horon da ‘yan wasan suka samu na watanni kalilan ne, sun lashe gasar. Haka ma a shekarar 2018, sun sake zama zakara.

A watan Nuwamban 2018, da taimakon kudi daga gwamnatin wurin, aka gina filin wasan kwallon kafa ga makarantar firamare ta Zhangpan. Daliban sun yi matukar farin ciki da suka yi ido biyu da kyakkyawan filin a karon farko.

Halartar gasar wasan kwallon kafa ta yara ta Ziri Daya da Hanya Daya a jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kanta dake arewacin kasar Sin a shekarar 2019, daya ne daga cikin abubuwan da ‘yan wasan ba za su manta da shi ba. Saboda kungiyar ta kusa rasa damar zuwa. Song yana son kungiyar ta halarci gasar ta kasa da kasa, amma makarantar ba za ta iya daukar nauyin kudin sufuri da na masauki ba. Sai dai saboda tallafin mashirya gasar, da ofishin kula da harkokin ilimi da wasanni na gundumar Mengjin, kungiyar ta samu damar halartar gasar. Matar Li Lei, wadda likita ce, ta bi su domin ba ‘yan wasan kulawa.

Yayin bikin bude gasar, ‘yan wasan sauran kungiyoyi sun sanya riguna da takalma iri daya dukkansu, yayin da ‘yan wasan daga makarantar Zhangpan suka sanya launika daban daban, haka ma takalmansu. Sai dai duk da haka, kungiyar ta doke kungiyoyi 15 da takara da su, ciki har da ta kasashen Mongolia da Rasha, har ma ta zama zakara a gasar na rukunin ‘yan wasan kasa da shekaru 12. A cewar Song, wannan ita ce gasa mafi daraja da kungiyar ta cinye.(Kande Gao)