logo

HAUSA

Kasar Sin ta fara shigo da naman rago daga nahiyar Afrika

2024-09-08 18:04:18 CMG Hausa

A yau Lahadi, hukumar kwastam ta birnin Changsha na lardin Hunan, ta bada izinin shigo da naman rago daga kasar Madagascar cikin kasar Sin. Wannan shi ne karo na farko da aka shigo da nama daga nahiyar Afrika kasar Sin, wanda ke zama wata muhimmiyar nasara ga cinikayyar nama tsakanin Sin da Afrika.

Za a sayar da naman a dakunan sayar da abinci daban-daban da manyan kantuna a fadin Hunan na tsakiyar kasar Sin, lardin dake kan gaba wajen cinikayya da kasashen Afrika, haka kuma lardi na farko da ya fara cinikayya da su.

A bara ne kasar Sin ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar cinikayyar naman rago da Madagascar yayin baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afrika karo na 3 da aka yi a birnin Changsha.

A watanni 7 na farkon bana, darajar amfanin gona daga nahiyar Afrika da aka shigar Hunan ta kai kimanin yuan miliyan 240, kwatankwacin dala miliyan 33.9, karuwar kaso 10.6 kan na bara.

Baya ga naman rago daga Madagascar, hukumar kwastam ta Changsha ta bada shaidar izinin shiga kasuwa ga rukunoni 24 na kayayyakin da ake kawowa daga Afrika zuwa kasar Sin. Kayayyakin sun hada da abinci ko naman ruwa daga kasashen Kenya da Tanzania da Cashew daga Guinea Bissau da busasshen borkono daga Rwanda da kuma basassun kananan kifi daga Kenya. (Fa’iza Mustapha)