Ana taimakawa daliban kasashen Afirka cimma burinsu na gudanar da harkokin kasuwancin kasa da kasa ta yanar gizo a birnin Yiwu
2024-09-08 16:37:30 CMG Hausa
Yiwu, birni ne dake lardin Zhejiang a gabashin kasar Sin, kuma shahararriyar cibiyar kasuwancin kananan hajoji a kasar. A halin yanzu, ana kara samun ’yan kasuwa da shugabannin kamfanonin kasashen Afirka da suke zuwa birnin, don karo ilimi kan kasuwancin kasa da kasa ta yanar gizo ta intanet.