logo

HAUSA

Sin da Amurka sun tattauna kan manufofi da batutuwan cinikayya

2024-09-08 17:53:58 CMG Hausa

Kwamitin kula da harkokin cinikayya na Sin da Amurka, sun yi taron mataimakan ministoci karo na biyu, jiya Asabar a Tianjin, inda suka yi tattaunawa cike da kwarewa kuma mai ma’ana kan batutuwan da suka shafi manufofi da cinikayya.

Wakilin kula da shawarwarin cinikayyar kasa da kasa, wanda kuma shi ne mataimakin ministan kula da cinikayya na kasar Wang Shouwen da mataimakiyar sakataren ma’aikatar kula da cinikayya da kasashen ketare na Amurka Marisa Lago ne suka jagoranci taron.

Da yake jawabi, Wang Shouwen ya ce a shirye kasar Sin take ta hada hannu da Amurka wajen karfafa tuntubar juna da fadada hadin gwiwarsu da shawo kan bambance-bambance da samar da kyakkyawan muhallin kasuwanci domin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Yayin taron, bangaren kasar Sin ya bayyana damuwar da yake da ita don gane da sashe na 301 na dokar haraji da sashe na 301 mai binciken bangaren kera jiragen ruwa na kasar Sin da sauran bangarori, da yadda Amurke ke wuce gona da iri wajen amfani da batun tsaron kasa, da takaita zuba jari tsakaninsu da matakan takaita cinikayyar kayayyaki da Amurka ke dauka kan Sin da rashin adalcin da ake nunawa kamfanonin Sin a Amurka da sauran batutuwa. (Fa’iza Mustapha)