logo

HAUSA

An gudanar da bikin kaddamar da sassakar tunawa da gasar Olympics ta Paris

2024-09-07 16:55:19 CMG Hausa

An gudanar da bikin kaddamar da sassakar tunawa da gasar Olympics ta birnin Paris na kasar Faransa, a jiya Juma’a 6 ga watan nan, a babban gidan Katara na birnin Grande Noissy, dake yankin Ile-de-France.

Kafar CMG ta kasar Sin ce ta bayar da kyautar sassakar, mai lakabin "Kasancewa a jirgin ruwa guda", ga kwamitin kula da wasannin Olympics da wasannin motsa jiki na Faransa. Baya ga kaddamar da sassakar, an kuma yi bikin kaddamar da kebantaccen dandalin wanzar da zaman lafiya na Olympic ko “Olympic Peace Park" duka a jiyan.

Da yake tsokaci game da hakan, babban daraktan CMG Shen Haixiong, ya aike da wasikar taya murnar gudanar da bikin, yana mai cewa, kaddamar da wannan kyauta ta dindindin, ta alamta cewa, kawancen Sin da Faransa na kara bunkasa a dukkanin yanayi mai dadi ko akasinsa, yana kuma kara tabbatar da muhimmin ruhin Olympic na wanzar da zaman lafiya, kawance da samar da ci gaba.

Kaddamar da kebantaccen dandalin wanzar da zaman lafiya na "Olympic Peace Park", a wurin da aka kafa sassakar, ya samar da karin alamar ruhin Olympic, da ingiza sadarwa, da tattaunawa ga birnin, wanda ya kasance cibiyar kafuwar gasar Olympic ta zamani.    (Saminu Alhassan)