logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Kaduna za ta hada kai da asusun UNICEF wajen ilimantar da yara dubu dari 2 da basa zuwa makaranta

2024-09-07 16:19:39 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya tare da hadin gwiwa da asusun UNICEF za su taimaka wajen shirin ilimantar da yara dubu dari 2 da basa zuwa makaranta a jihar.

Mataimakiyar gwamnan jihar Dr. Hadiza Balarabe ce ta tabbatar da hakan ranar juma’a 6 ga wata yayin bikin sanya hannu kan yarjejeniyar a gidan gwamnatin jihar dake garin Kaduna.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Dr. Hadiza Balarabe ta ce manufar shirin shi ne tabbatar da ganin dukkan kananan yaran jihar sun samu ilimi ingantacce ba tare da la’akari da matsayin da suke ba.

Ta ce hakika shirin zai kasance wata ‘yar manuniya da za ta sauya al’adar cire yara daga makarantu da wasu iyaye ke yi musamman yara mata, da kuma gaza sanya yaran da suke da nakasa da yara marasa galihu makaranta, inda ta kara da cewa, irin wadannan rukuni na yara, gwamnati na da burin ba su ilimi da damammaki domin su sami hasken rayuwa.

Mataimakiyar gwamnan jihar ta Kaduna ta ce, suna fatan shirin zai kai ga samun nasarar mayar da sama da yara dubu dari 2 makaranta, sannan kuma sama da daliban makarantun firamare miliyan 1 da dubu dari 2 ne za su amfana da kayayyakin karatu, haka kuma malamai sama da dubu 36 da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi ne za a baiwa horon samu karin kwarewar aiki a jihar ta Kaduna.(Garba Abdullahi Bagwai)