Wang Yi ya gana da jakadan Amurka kan sauyin yanayi
2024-09-07 16:08:36 CMG Hausa
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da babban mashawarcin shugaban kasar Amurka kan batun sauyin yanayi tsakanin kasa da kasa John Podesta a jiya Asabar.
Yayin zantawar tasu, Wang ya ce, cudanyar shekaru 45 ta tabbatar da bukatar dake akwai ta kasancewar Sin da Amurka kawayen juna maimakon abokan adawa. Kaza lika, kamata ya yi sassan biyu su baiwa juna damar cimma burikansu, maimakon zama masu kazamar takara tsakani.
Ya ce, tawagogin kasashen biyu masu lura da batun sauyin yanayi, sun ci gaba da tattaunawar kut da kut, tare da cimma sakamakon hadin gwiwa na zahiri cikin wannan shekara da muke ciki. Burin shi ne bangaren Amurka ya samar da daidaiton manufofi, da martaba batutuwan da Sin ke mayar da martani a kansu, da kaucewa baiwa kasuwa kariya, da amfani da batun tsaro ta hanyoyin da ba su dace ba, da hada hannu da Sin wajen magance kalubalolin da duniya ke fuskanta.
A nasa bangare kuwa, mista Podesta cewa ya yi, hadin gwiwa a fannin magance matsalar sauyin yanayi, muhimmiyar matsaya ce da shugabannin kasashen biyu suka cimma, kana jigo ne cikin manufofin dangantakar kasashen biyu, kuma batu ne mai nasaba da tsarin gudanar hadin gwiwar sassan kasa da kasa.
Mista Podesta ya kara da cewa, bangaren Amurka a shirye yake ya karfafa tattaunawa da aiwatar da tsare-tsare tare da Sin, kana da shiga hadin gwiwa mai ma’ana tsakaninsu. (Saminu Alhassan)