logo

HAUSA

Ta yaya Sin da Afirka za su ci moriyar juna ta fuskokin tattalin arziki da kasuwanci?

2024-09-07 17:31:00 CMG Hausa

An gudanar da babban taron shugabannin kamfanonin kasar Sin da kasashen Afirka karo na 8, jiya Jumma’a 6 ga wata a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Baya ga wakilan kamfanonin kasar Sin, akwai kuma wakilan kamfanonin kasashen Afirka 48 da suka halarci taron, ciki har da na Senegal, da Afirka ta Kudu, da Kenya da sauransu, masu alaka da sana’o’i daban-daban.

A wajen bikin kaddamar da taron, firaministan kasar Sin Li Qiang ya ba da shawarar cewa, ya dace Sin da Afirka su kara tuntubar juna ta fannin kasuwa, da kara yin mu’amalar sana’o’insu, da kuma kara karfin kirkire-kirkire.

A wajen taron kolin dandalin FOCAC na wannan karo, wato dandalin tattuna hadin-gwiwar Sin da Afirka, kasar Sin ta ce, za ta hada kai tare da kasashen Afirka, don daukar wasu manyan matakan abokantaka guda 10 don zamanantar da kansu, inda a wannan sabon mafari, kamfanonin Sin da Afirka za su fuskanci karin damammakin hadin-gwiwa.

Ana samun damammaki daga mu’amalar tsare-tsaren sana’o’i iri-iri, al’amarin da ya kasance tushen hadin-gwiwar tattalin arziki da kasuwanci. Sin babbar kasa ce dake tasowa, wadda ke da cikakken tsarin sana’o’i iri-iri a duk fadin duniya, kana, Afirka, nahiya ce dake da dimbin kasashe masu tasowa da yawa a duniya. Don haka, bangarorin biyu za su iya yin hadin-gwiwa a tsarin sana’o’i da tsarin samar da kayayyaki.

Ana kuma samun damammaki da dama ta hanyar tattaro sabon kuzari. Tun daga habaka “kasuwancin hanyar siliki” cikin hadin-gwiwa, har zuwa motoci masu amfani da sabon makamashi, da na’urorin hasken rana, da na’urorin samar da wutar lantarki bisa karfin iska da kasar Sin ta kera, wadanda suka taimaka sosai ga ci gaban sabbin makamashi a Afirka, kasar Sin da kasashen Afirka suna gudanar da hadin-gwiwa sosai a fannonin tattalin arziki irin na zamani, da samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba.

A cewar shugabannin kamfanonin Afirka da suka halarci taron, babban abun dake tattare da hadin-gwiwar Afirka da Sin shi ne yin kirkire-kirkire, kuma dabarun kasar Sin ta fannin sabon makamashi, da kera motoci masu amfani da lantarki sun cancanci Afirka ta yi koyi.

Kaza lika, ana samun damammaki daga ra’ayi iri daya da aka cimma wajen yin hadin-gwiwa. A wajen babban taron shugabannin kamfanonin kasar Sin da kasashen Afirka karo na 8, shugabannin kamfanonin sun nuna matukar sha’awarsu ta karfafa hadin-gwiwa, al’amarin dake da babbar ma’ana, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar kalubalen ra’ayin ba da kariya, tare da samar da kuzari ga duniya wajen cimma moriya tare. (Murtala Zhang)