Xi ya bukaci aiwatar da matakan saukaka tasirin ibtila’i bayan da mahaukaciyar guguwar Yagi ta aukawa kudancin Sin
2024-09-07 20:23:59 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci da a aiwatar da matakan saukaka tasirin ibtila’i, bayan da mahaukaciyar guguwar nan ta Yagi ta aukawa kudancin Sin.
Yagi, ita ce mahaukaciyar guguwa ta 11 da ta auku a bana, inda ta shafi wasu sassa na lardunan Hainan da Guangdong a jiya Juma’a, tare da hallaka mutane 3 da jikkata wasu 95.
Shugaba Xi, ya bukaci a aiwatar da dukkanin matakai na tabbatar da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu. Kaza lika, ya bukaci a aiwatar da matakan ceto, da kyautata tsugunarwa, da sauyawa wadanda ibtila’in ya shafa matsugunai. Har ila yau, a dakile aukuwar tasirin guguwar a mataki na biyu, tare da yin duk mai yiwuwa wajen saukaka asarar da za ta haifar.
Bugu da kari, shugaban na Sin ya bukaci a gaggauta gyara ababen more rayuwa, ciki har da na sufuri, da wutar lantarki da turakun sadarwa, da gudanar da ayyukan farfado da wurare bayan aukuwar bala’i, ta yadda za a sake dawo da yanayin rayuwar al’umma da ayyukansu cikin sauri.
Rahotanni na cewa, mahaukaciyar guguwar Yagi, ta shafi sama da mutane miliyan 1.2 a lardunan Hainan, da Guangdong da jihar Guangxi, ta kuma haifar da daukewar wutar lantarki da sadarwa ga jama’a da dama, tare da rusa tarin gidaje.
Yanzu haka, an kai ga dawo da hidimomin sadarwa da wutar lantarki a wasu wuraren. (Saminu Alhassan)