An cimma nasarori masu yawa kan hadin gwiwar nazarin yanayi tsakanin Sin da Afirka
2024-09-06 13:36:26 CMG Hausa
A karkashin tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC, da na shawarar “ziri daya da hanya daya”, Sin da kasashen Afirka sun gudanar da hakikanin hadin gwiwa ta fuskar nazarin yanayi a dukkan fannoni. Yanzu, an samu jerin nasarori masu yawa bisa ga irin hadin gwiwar a fannonin ababen more rayuwa, da tsarin ba da gargadin gaggawa a lokacin farko, da amfani da tauraron dan adam na binciken yanayi na Fengyun da dai makamantansu.
A halin yanzu, kasar Sin ta aiwatar da ayyukan gina kayayyakin more rayuwa a bagaren binciken yanayi a kasashen Afirka kamar Zimbabwe, da Kenya, da Namibiya, da Kamaru, da Sudan, da Guinea da dai sauransu, wadanda suka hada da kafa tashoshin binciken yanayi, da tsarin lura da yanayi na dan Adam, da tsarin karbar bayanan tauraron dan adam FY-3 da dai sauransu, ta hakan aka inganta kwarewar kasashen ta fannonin hasashen yanayi da rigakafi da tinkarar bala’u.
Bugu da kari, kasar Sin ta ba da horo na gajeren lokaci da na dogon lokaci ga mutane 3963 da suka fito daga kasashen Afirka 52 kan batutuwan da suka hada da tauraron dan adam na binciken yanayi da ma sauyin yanayi da sauransu. (Bilkisu Xin)