logo

HAUSA

Shugaban Najeriya: Ci gaban duniya ba faduwar wani tashin wani ba ne

2024-09-06 11:33:47 CMG Hausa

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya bayyana jiya Alhamis cewa, nasarar da aka samu a dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, ya nuna cewa a ci gaban duniya babu batun hadin gwiwa ta faduwar wani tashin wani.

Tinubu ya bayyana hakan ne a wajen bikin bude taron kolin FOCAC na shekarar 2024, inda ya kara da cewa, hadin gwiwar kasashen Afirka da kasar Sin ta tsaya daram, duk da kalubalen da duniya ke fuskanta a fannin tattalin arziki da matsalolin yankuna. Yana mai ba da misali mai karfi na sakamakon da za a iya samu ta hanyar mutunta 'yancin kai, da rashin tsangwama.

Tinubu ya kara da cewa, "Kasar Sin ta ci gaba da nuna aniyarta ga Afirka, ba wai ta hanyar tallafin kudi da raya kasa kadai ba, har ma ta hanyar musayar al'adu da ke kara kusancin jama'armu." 

Ya kuma yi kira da a kara yin kokarin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, wajen hada karfi da karfe, da samar da ci gaban da ba a taba ganin irinsa ba, da kuma cimma babban matsayi na hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da Sin a cikin shekaru masu zuwa. (Mohammed Yahaya)