Dangantaka da kasar Sin ta bada gudunmuwa ga bunkasar tattalin arziki da zamantakewa a Nijeriya
2024-09-06 13:53:38 CMG Hausa
Gwamnatin Nijeriya ta bayyana hadin gwiwar cinikayya da kasar Sin a matsayin wanda ya taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da zamantakewa a kasar, tare da inganta fahimtar juna da abota da musayar al’adu da ma fasahohin tsakanin al’ummominsu.
Ministar kula da cinikayya da zuba jari da masana’antu ta Nijeriya, Dr. Doris Uzoka- Anite, wadda ke birnin Beijing domin halartar taron dandalin FOCAC ce ta bayyana haka, yayin zantawarta da sashen Hausa na CGTN wakiliyarmu Fa’iza Muhammad Mustapha.
Dr. Doris Anite ta kara da cewa, zuwan shugaban Nijeriya Bola Tinubu da tawagarsa kasar Sin, ya nuna yadda Nijeriyar ke daukar dangantakarta da Sin da muhimmanci da kuma yadda take fatan zurfafa hadin gwiwarsu a dukkan bangarori.
Ta ce tasirin dangatakar kasashen kan tattalin arziki da zamantakewa na da muhimmanci matuka, tana mai cewa, kasar za ta kara fadada bude kofarta ga karin Sinawa masu zuba jari don kafawa ko habaka sana’o’insu a kasar.
Da take tsokaci game da ajandar kasar ta bunkasa ayyukan masana’antu da kere-kere, ta ce bisa la’akari da gogewar kasar Sin da kuma dimbin nasarorin da ta samu a wannan bangare, Nijeriya na da abubuwa da dama da za ta iya koyo daga gare ta.
“Kasar Sin ta samu dimbin nasarori a wannan bangare, har ta kai matsayin kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya. Akwai abubuwa da dama da za mu iya koya daga gogewarsu, kuma abu mafi muhimmanci shi ne za mu kara bude kofarmu ga karin Sinawa masu zuba jari.”
Ministar ta kara da cewa, a matsayin Nijeriya na wadda ke da muhimmanci a nahiyar Afrika da dimbin albarkatu da matasa masu jini a jika da take da su, masu zuba jari na kasar Sin za su samu babbar kasuwa dake da karfi da dimbin damarmakin samun riba, lamarin da zai kai ga amfanawa bangarorin biyu.
“Sinawa masu zuba jari dake Nijeriya sun samu nasarori, muna son kara bude kofarmu gare su. Yanzu kasar Sin na karkata ga manufar sabon karfin samar da hajoji, akwai wasu bangarorin da za su iya kafa sansanoninsu a Nijeriya. Nijeriya wuri ne mai muhimmanci, muna son mayar da hankali kan fitar da kayayyakin da aka riga aka sarrafa, ta hanyar amfani da albarkatu da ma’aikata da muke da su. bisa la’akari da matsayinmu a yankin ciniki mara shinge na nahiyar Afrika, ba kasuwar Nijeriya mai mutane sama da miliyan 250 kadai za su shiga ba, har da babbar kasuwa mai mutane biliyan 1.3. Kasuwa ce sabuwa dake da karfi da dimbin damarmaki.”
Bugu da kari, ta ce daya daga cikin manufar ziyararsu a kasar Sin ita ce, kara tabbatar wa masu zuba jari tsaron rayuka da dukiyoyinsu da kyayyawan muhallin kasuwaci da ingantattun manufofi da dabarun saukaka ayyukansu da Nijeriya ta tanada.
Har ila yau, ministar ta ce akwai sabbin bangarorin da dama da kasashen biyu za su kara hadin gwiwa, wandanda za su samar da moriyar juna. (Fa’iza Mustapha, Safiyah Ma)