Peng Liyuan ta zanta da Uwargidan Shugaban Kongon Brazzaville
2024-09-06 15:23:08 CGTN Hausa
Yau da safe, uwargidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan ta zanta tare da shan shayi tare da takwararta ta kasar Kongon Brazzaville Antoinette Sassou-Nguesso.
Madam Peng ta jinjinawa Madam Antoinette kan kokarin da ta dade take yi ta fannin kiwon lafiya a Afirka. A nata bangare kuwa, Antoinette ta nuna godiya ga Madam Peng kan tallafi mai daraja da kasar Sin musamman ma Madam Peng ta baiwa kasashen nahiyar a bangaren kiwon lafiyar jama’arsu, da kuma raya sha’anin mata da yara. (Amina Xu)