Xi ya gana da shugaban Gambia
2024-09-06 20:37:18 CMG Hausa
Da yammacin yau Juma’a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na Gambia Adama Barrow, wanda ya zo birnin Beijing don halartar taron FOCAC na bana. Yayin ganawar tasu, shugabannin biyu sun sanar da daga alakar kasashensu zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare.
Shugaba Xi, ya ce alakar Sin da Gambia ta ci gaba da samun tagomashi a shekarun baya-bayan nan. Kaza lika, sassan biyu sun kara yaukaka amincewa juna ta fuskar siyasa, tare da cimma nasarori a fannonin hadin gwiwa na zahiri. Har ila yau, sassan biyu sun zamo sahihan kawaye, kuma abokan hulda na hakika kan turbar samar da ci gaba, da kara farfado da kansu.
Bugu da kari, shugaba Xi ya ce kamata ya yi Sin da Gambia su ci gaba da goyon bayan juna, kan batutuwan da suka shafi manyan moriyarsu, da abubuwa da suke mayar da hankali kansu, kana su kara karfafawa, da kare kawancensu, da amincewa junansu, da ingiza ci gaban alakarsu, bisa daidaito kuma cikin tsawon lokaci.
A wani ci gaban kuma, shugaba Xi ya tattauna da shugaban majalissar gwamnatin sojin Sudan Abdel Fattah Al-Burhan, da shugaban Madagascar Andry Nirina Rajoelina, da na Sudan ta kudu Salva Kiir, da na jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera. (Saminu Alhassan)