Ministan harkokin waje kasar Sin ya ce an samu cikakkiyar nasara a taron FOCAC na shekara 2024
2024-09-06 09:54:02 CMG Hausa
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a jiya Alhamis cewa, an samu cikakkiyar nasara a taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC na shekarar 2024.
Wang, wanda kuma mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai tare da ministan harkokin wajen Senegal Yacine Fall, da ministan harkokin wajen jamhuriyar Congo Jean-Claude Gakosso.
Da yake karin haske kan manyan sakamako da aka cimma a taron, Wang ya ce, an daukaka dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka dake da huldar diflomasiyya da kasar Sin zuwa matsayin dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare. Kana, an daga darajar dangantakar Sin da Afirka baki daya zuwa wata al'ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya a dukkan fannoni na sabon zamani.
A nasu bangare kuwa, Falla da Gakosso cewa suka yi, hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da Sin ya sauya makomar Afirka, kuma ko shakka babu zai shiga tarihi a matsayin abin koyi na hadin gwiwar kasa da kasa. (Mohammed Yahaya)