Sin ta gabatarwa Canada bukatar yin tattaunawa a WTO don gane da batun karin haraji
2024-09-06 20:27:58 CMG Hausa
Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ya ce a Juma’ar nan Sin ta gabatarwa kasar Canada bukatar gurfana gaban kungiyar cinikayya ta duniya WTO, game da shirin Canadan na kakabawa ababen hawa masu amfani da lantarki kirar kasar Sin, da karafa da goran ruwa na Sin karin haraji.
Jami’in ya ce, Canada ta yi watsi da ka’idojin WTO, da alkawarinta na biyayya ga kungiyar, inda ta tsara dorawa ababen hawa kirar kasar Sin masu amfani da lantarki karin harajin kaso 100, da kaso 25 kan karafa da goran ruwa da Sin din ke shigarwa kasar, matakin da ya zamo bin ra’ayin kashin kai ne, da kuma baiwa kasuwa kariya.
Kaza lika, hakan zai yi matukar gurgunta tsarin gudanar da cudanyar cinikayya tsakanin bangarori daban daban, da lalata tsarin ayyukan masana’antu na shigar da ababen hawa masu aiki da lantarki, da karafa da goran ruwa kirar kasar Sin zuwa dukkanin sassan duniya, matakin da ko kadan Sin ba za ta lamunta ba. (Saminu Alhassan)