An zartas da hadaddiyar sanarwa game da zurfafa hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka bisa tsarin shawarar ci gaban duniya a taron koli na FOCAC
2024-09-06 14:37:25 CMG Hausa
An gudanar da taron koli a sabon zagaye, na dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a tsakanin ranekun Laraba zuwa yau Juma’a a nan birnin Beijing, inda gaba daya mahalarta taron suka amince da bayar da hadaddiyar sanarwa, game da zurfafa hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka bisa tsarin shawarar ci gaban duniya.
Mahalarta taron suna ganin cewa, shawarar ci gaban duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, ta zo daidai da ajandar neman dauwamammen ci gaba ta MDD nan da shekarar 2030, da ajandar Tarayyar Afirka kafin shekarar 2063, da kuma manufofin ci gaba bisa manyan tsare-tsare na kasashen Afirka. Kana ta kara azama kan neman ci gaban duniya tare.
A daya bangaren kuma, mahalarta taron sun bayyana fatansu, na ganin an kara bunkasa hadin kai bisa manyan tsare-tsare, karkashin shawarar ci gaban duniya, da zurfafa bunkasuwa da hadin gwiwa, da kuma gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga Sin da Afirka a ko da yaushe a sabon zamani. (Bilkisu Xin)