logo

HAUSA

Xi Jinping Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Kongon Brazzaville

2024-09-06 14:32:43 CGTN Hausa

 

Da safiyar yau Juma’a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Kongon Brazzaville Denis Sassou-Nguesson, wanda ke halartar taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka FOCAC, tare da ziyarar aiki a nan birnin Beijing.

Yayin ganawar ta su, shugaba Xi ya taya Sassou murnar karbar jagorancin bangaren kasashen Afirka masu halartar FOCAC a karo mai zuwa, kuma ya jinjinawa gudunmawar da mista Sassou ya bayar ga taron na wannan karo.

A nasa bangare, shugaba Sassou ya yi godiya ga goyon bayan da Sin take baiwa Kongon Brazzaville, tare da fatan kara hadin gwiwa da Sin, wajen tabbatar da ci gaban da aka samu a wannan karo.

Ban da wannan kuma, Xi ya gana da shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mahmud, da na Liberiya Joseph Nyumah Boakai, da na Burundi Evariste Ndayishimiye, da dai sauran shugabannin kasashen Afirka. (Amina Xu)