logo

HAUSA

Na’urar gwaji ta binciken sararin samaniya ta Sin da ake iya sake yin amfani da ita ta sauka kasa cikin nasara

2024-09-06 11:10:59 CMG Hausa

Na’urar gwaji ta binciken sararin samaniya ta Sin da ake iya sake yin amfani da ita, wadda aka harba a cibiyar harbar tauraron dan Adam ta Jiuquan ta kasar Sin, ta yi tafiya a sararin samaniya har na tsawon kwanaki 268, kuma ta dawo doron kasa a yau ranar 6 ga wata cikin nasara. An kuma yi gwajin cikin nasara, wannan ya alamta cewa, Sin ta raya fasahohin na’urorin binciken sararin samaniya da ake iya sake yin amfani da su yadda ya kamata, a nan gaba za a samar da sauki ga hanyoyin kai komo daga sararin samaniya don binciken sararin samaniya cikin lumana. (Zainab Zhang)