logo

HAUSA

Yadda tashar jiragen ruwa ta Kribi ta kasar Kamaru ke tallafawa al’ummomin wurin

2024-09-05 10:03:06 CMG Hausa

A yayin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka na shekarar 2018, wanda aka gudanar a birnin Beijing, shugaba Xi Jinping ya ba da jawabi cewa, kasar Sin ta tsai da kudurin yin hadin gwiwa da kungiyar tarayyar kasashen Afirka wato AU wajen tsara “shirin hadin gwiwar ababen more rayuwa na Sin da Afirka”. Tun daga shekarar 2013, ya zuwa yanzu, kasar Sin ta ba da taimako ga kasashen Afirka wajen gina layukan dogo sama da kilomita dubu 6, da manyan hanyoyin mota sama da kilomita dubu 6, da manyan na’urorin samar da wutar lantarki sama da guda 80, da kuma tasoshin jiragen ruwa kimanin guda 20. Cikin shirinmu na yau, bari mu ga yadda tashar jiragen ruwa ta Kribi ta kasar Kamaru ke tallafawa al’ummomin wurin. (Maryam)