Shugaban Sin ya gana da shugabannin Ghana da Namibiya da Rwanda da Guinea Bissau gami da firaministan Sao Tome da Principe
2024-09-05 21:27:06 CMG Hausa
Da maraicen yau Alhamis 5 ga watan Satumba, a babban dakin taron al’umma dake Beijing, fadar mulkin kasar Sin, shugaban kasar Xi Jinping, ya yi shawarwari tare da shugabannin wasu kasashen Afirka da suka shigo kasar don halartar taron FOCAC, wato dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka, ciki har da shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo, da firaministan kasar Sao Tome da Principe, Patrice Trovoada, da shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, inda shugabannin suka sanar da daga dangantakarsu da kasar Sin zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare.
Shugaba Xi ya ce, kasar Sin na fatan yin kokari tare da kasar Ghana, don fadada hadin-gwiwa a fannonin noma, da kamun kifi, da makamashi da ma’adinai, da ababen more rayuwar al’umma da sauransu. Kaza lika, kasar Sin za ta ci gaba da marawa kasar Sao Tome da Principe baya, wajen gina kasa da habaka tattalin arziki, ta yadda dangantakar kasashen biyu za ta amfani al’ummar Sao Tome da Principe. Sai dai kuma, kasar Sin tana goyon-bayan kasar Rwanda wajen bin tafarkin ci gaba cikin ‘yanci, da kara samun fahimtar juna ta fannin siyasa tare da Rwanda, da habaka ra’ayi iri daya tsakaninsu, don tafiya kafada da kafada bisa tafarkin zamanantar da kasashensu.
A wannan rana kuma, shugaba Xi ya yi shawarwari tare da shugabannin kasashen Namibiya da Guinea Bissau, wato Nangolo Mbumba da Umaro Cissoko Embalo. Xi ya ce, kasarsa na fatan yin kokari tare da Namibiya da sauran kasashen Afirka, don aiwatar da manyan nasarorin da aka samu a taron kolin na wannan karo a zahiri, da neman ci gaba tare, don kara gina al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya. Bugu da kari, Sin na fatan karfafa zumunci tare da Guinea Bissau, da habaka hadin-gwiwarsu bisa manyan tsare-tsare, da kiyaye cikakken ’yanci, da tabbatar da tsaro da muradun ci gaba na kasashensu. (Murtala Zhang)