logo

HAUSA

Xi Jinping ya gana da António Guterres

2024-09-05 15:41:42 CGTN Hausa

 

Yau da tsakar rana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da babban sakataren MDD António Guterres, wanda ke halartar taron kolin dandalin tattauna kan hadin kan Sin da Afirka FOCAC da  ke gudana a nan birnin Beijing.

Xi ya ce, Sin na daukar bunkasuwar huldar Sin da Afirka da muhimmanci. Sin ba ta nufin cin moriya ta kanta kawai a hadin gwiwarta da Afirka. Sin na fatan kara hadin kai da MDD don taka rawar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da ma farfado da nahiyar Afirka.

Ban da wannan kuma, Xi ya jadadda goyon bayanta ga MDD a harkokin duniya, kuma matakin ya zama ka’ida da Sin ta nace a tafiyar da harkokin diplomasiyya.

A nasa bangare, António Guterres ya ce, hadin gwiwar Sin da Afirka na taka rawa wajen rage rashin daidaito da Afirka take fuskanta, da ma taimakawa Afirka wajen tabbatar da samun bunkasuwa cikin lumana. MDD na fatan kara hadin gwiwarta da Sin, don gaggauta daidaita harkokin duniya cikin adalci da daidaici, da ma kafa kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya. (Amina Xu)