Sin ta bukaci Amurka da ta dage dukkanin karin haraji kan hajojinta
2024-09-05 20:48:50 CMG Hausa
Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin He Yongqian, ya ce kasarsa na fatan Amurka za ta gyara kuskurenta, tare da gaggauta dage dukkanin karin haraji da ta dora kan hajojin kasar Sin.
He Yongqian, ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayar manema labarai a Alhamis din nan, game da jan kafar da Amurka ke yi a baya-bayan nan, game da bayyana matsaya kan karin haraji da ta kakabawa hajojin Sin karkashin sashen doka na 301.
Tuni dai kungiyar cinikayya ta duniya WTO, ta tabbatar da cewa sashen na 301 ya sabawa ka’idojin kungiyar, don haka a cewar jami’in na Sin matakin Amurka na kara haraji kan hajojin Sin ba abun da zai haifar sai kara dagula al’amura.
Kafin hakan, ofishin wakiliyar cinikayyar Amurka ya nemi jin ra’ayoyin al’umma don gane da tanadin sashen na 301 mai nasaba da karin haraji, inda kaso mafi yawa ko dai sun soki lamirin hakan, ko sun bukaci a fadada hajojin da za a janyewa harajin.
Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayyar ta kasar Sin ya kara da cewa, hakan ya nuna tanadin karin haraji karkashin wannan sashe na 301, bai samu karbuwa tsakanin al’ummun kasar Amurka ba. (Saminu Alhassan)