logo

HAUSA

Wakilin kasar Sin ya yi kira da a kara kokarin diflomsiyya don dakile yakin Gaza cikin gaggawa

2024-09-05 10:29:28 CMG Hausa

A ranar 4 ga watan Satumba, agogon wurin, kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya gudanar da taro kan hali da ake ciki tsakanin Falasdinu da Isra’ila. Inda mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya sake nanata kira da a kara himma a fannin diflomasiyya don sai kaimi ga sako da dawo da dukkan wadanda ake tsare da su cikin gaggawa, walau Isra’ilawa ko Falasdinawa.

Geng Shuang ya bayyana cewa, mutuwar fursunoni shida a zirin Gaza abin takaici ne matuka, da nuna juyayi, kuma Sin ta yi Allah wadai da duk wani cin zarafi da ake yi wa fararen hula.

Geng Shuang ya kara da cewa, kamata ya yi shugabannin Isra'ila su saurari kakkausar muryar jama'a, su ba da fifiko wajen ceto mutanen da ake tsare da su, da kuma ceto rayukan jama'a, da kuma yin iyakacin kokarinsu wajen cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kawo karshen yakin. Ya kamata kasashen da ke da tasiri sosai kan bangarorin da abin ya shafa su kuma rungumi dabi'ar bayyana gaskiya da rikon amana tare da daukar kwararan matakai don dakile yakin Gaza.

Geng Shuang ya kuma bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan kwamitin sulhu na MDD wajen kara daukar matakai na sa kaimi ga aiwatar da shawarwarin da suka dace, da dakile yakin da ake fama da shi cikin gaggawa, da kawar da bala'o'in jin kai. (Yahaya)