Kamaru ta bayyana sunayen ‘yan wasa 24 da za su buga mata wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin AFCON tare da Namibia
2024-09-05 20:55:33 CMG Hausa
Babban kocin kungiyar kwallon kafar kasar Kamaru Marc Brys, ya gabatar da sunayen ‘yan wasan tawagar kasar su 24, wadanda za su bugawa kasar wasan farko na neman gurbin buga gasar cin kofin kwallon kafa na Afirka ko AFCON tare da kasar Namibia.
‘Yan wasan sun hada da Andre-Frank Zambo Anguissa, da Andre Onana, da Bryan Mbeumo, da Vincent Aboubakar. Kamaru za ta karbi bakuncin Namibia a wasan da za su fafata ranar 7 ga watan nan, yayin da tuni kungiyar kasar ko “Indomitable Lions” ta riga ta fara atisaye tun a karshen makon jiya.
Wani mai sharhi kan harkokin wasanni dan kasar Kamaru mai suna James Malu, ya ce hukumar wasan kwallon kafar kasar wato Cameroon FA, da ma’aikatar wasannin kasar na da sabani kan wanda ke da karfin iko game da kungiyar ta “Indomitable Lions”. Wannan lamari ya haifar da babban kalubale, har ta kai ba a san wurin da za a buga wasan dake tafe ba. Ya ce ma’aikatar wasannin na son a buga wasan a birnin Yaounde fadar mulkin kasa, yayin da FA ta sanar da shirin buga wasan a garin Garoua. Don haka a cewar Malu, wannan yanayi na ja-in-ja na iya shafar kwazon kungiyar yayin wasan dake tafe.
A wasannin neman gurbin buga gasar cin kofin na Afirka, Kamaru na a rukunin J, tare da Namibia, da Kenya, da Zimbabwe. Tuni kuma aka tsara gudanar da gasar ta AFCON ta 35 a shekara mai zuwa a kasar Morocco.
Bayan lashe kofin Europa koci Luis De la Fuente ya sanar da sabbin ‘yan wasan kungiyar kwallon kafar Sifaniya
Bayan ya jagoranci kasar Sifaniya zuwa lashe kofin kasashen turai na European Championship a kakar bana, kocin kungiyar kwallon kafar Sifaniyan Luis de la Fuente, ya ayyana wasu sabbin ‘yan wasa da ya sanya cikin jerin ‘yan wasan farko na Sifaniya.
Yayin da Sifaniya ke shirin fafatawa da Serbia, da Switzerland a gasar UEFA Nations League, koci De la Fuente ya kira dan wasan tsakiya mai bugawa Valencia wasa wato Pepelu. Kaza lika, ya kira Oscar Mingueza mai tsaron bayan Celta Vigo, da dan wasan gefe na Villarreal Yeremi Pino, da mai tsaron bayan Aston Villa Pau Torres, da kuma Aleix Garcia, wanda a baya yake cikin tawagar farko ta ‘yan wasan Sifaniya da suka buga European Championship, amma ya rasa damar buga wasan karshe.
Har ila yau, kocin ya sake kiran Jesus Navas na Sevilla bayan ya yi ritaya daga buga kwallon kafar kasa da kasa, sakamakon rauni da Alvaro Morata ya ji.
UEFA ta dakatar da dan wasan Sifaniya Rodrigo Hernandez daga buga wasa a Belgrade a ranar Alhamis, shi da Morata, bayan samun su da laifin furta kalaman da suka sabawa doka game da yankin “Gibraltar”, yayin bikin murnar lashe kofin “European Championship”, amma ana sa ran Hernandez din zai je Geneva domin bugawa Sifaniya wasan da za ta fafata tare da Switzerland a ranar 8 ga wata.
Bugu da kari, kocin ya kira mai tsaron ragar Chelsea Robert Sanchez, a matsayin mai tsaron gidan farko, yayin da Unai Simon ke farfadowa daga aikin da aka yi masa, wanda zai hana shi buga wasa har zuwa karshen shekarar nan.
Australia ta sanar da ‘yan wasan da za su buga mata wasannin neman gurbin buga gasar cikin kofin duniya na FIFA
Australia ta sanar da ‘yan wasa 24 da za su buga mata wasannin zagaye na 3, na neman gurbin buga gasar cikin kofin duniya na FIFA na shekarar 2026.
Kocin kungiyar kwallon kafar kasar Graham Arnold ne ya sanar da ‘yan wasan da za su takawa kasar leda, a wasan watan nan na Satumba da kasashen Bahrain da Indonesia, a gabar da karin ‘yan wasan Australian ke dawowa bayan fama da jinya.
Craig Goodwin, ya kammala jinyar ciwon da ya ji a kirji, wanda ya hana shi bugawa kasar sa wasa da Bangladesh da Palestine a watan Yuni, yayin da kuma dan wasan gefe Al Wehda ke kara zama muhimmin mataimaki wajen cin kwallaye, bayan da ya ciwa kungiyarsa kwallo 2 a wasannin farko 2 da ya buga na gasar Saudi Pro League a kakar bana.
Karin ‘yan wasan Australia da za su taka rawar gani sun hada da kyaftin din kungiyar ta “Socceroos”, kuma mai tsaron gida na farko Mat Ryan, wanda tuni ya sanya hannu kan kwangilar buga wasanni tare da kungiyar Roma ta Italiya a watan Yuli, shi ma ya koma wasa bayan ya dan yi hutu a watan Yuni. Akwai kuma mai tsaron baya Lewis Miller, da dan wasan tsakiya Aiden O'Neill wadanda dukkanin su ke buga wasa a turai, a yanzu sun koma kungiyar ta Australia bayan da suka rasa damar buga wasannin watan Yuni sakamakon rauni da suka yi. Kari kan hakan, akwai matashin dan wasan Bayern Munich Nestory Irankunda mai shekaru 18, wanda ya dawo taka leda bayan fama da rauni.
Baya ga kasashen Bahrain da Indonesia, kungiyar “Socceroos” za ta fafata tare da kasashen Sin, da Japan, da Saudiyya a rukuni na C na gasar AFC zagaye na 3. Daga bisani kungiyoyi 2 dake kan gaba a rukunin za su samu damar halartar gasar cin kofin duniya na 2026, yayin da kungiyoyin da suka zamo na 3 da na 4 za su kara buga wasan fitar da gwani, kafin samun gurbin buga babbar gasar ta kasa da kasa.
Yanzu kasa dai kungiyar “Socceroos” ta Australia na neman damar buga gasar cin kofin duniya na FIFA a karo na 6 a jere.
An gudanar da musayar ‘yan wasa gabanin rufe kasuwar cinikayya ta Premier League
Dan wasan kungiyar Chelsea Raheem Sterling ya koma Arsenal rance, gabanin rufe damar musayar ‘yan wasa dake buga gasar Premier Ingila.
Sterling mai shekaru 29 ya nemi komawa Arsenal ne bayan sabon kocin Chelsea Enzo Maresca, ya tabbatar da cewa dan wasan ba ya cikin rukunin farko na masu takawa kungiyar leda. Yanzu haka dai Sterling zai kasancewa Arsenal karin karfi na ‘yan wasan gaba masu cin kwallo.
Har ila yau, Chelsea ta dauko dan wasan gefe na Manchester United Jadon Sancho kafin a rufe damar hakan. Sancho ya koma Stamford Bridge rance, tare da sharadin Chelsea za ta amince ta tabbatar da komawarsa can didindin.
Sancho mai shekaru 24 a duniya, ya fuskanci sabani da kocin Manchester United Erik ten Hag, wanda hakan ya sa ya shafe rabin kakar bara yana takawa Borussia Dortmund kwallo a matsayin rance. Duk da cewa ya sake komawa yin atisaye tare da United gabanin fara buga wasannin kakar bana, ta bayyana a fili cewa koci Ten Hag na son ya bar kungiyar.
A daya bangaren kuma, ita ma kungiyar Manchester United ta daddale kwagila tare da dan wasan tsakiya na kasar Uruguay Manuel Ugarte, inda ya kammala komawa Manchester United daga Paris Saint-Germain. Ugarte ya isa birnin Manchester, inda ya shafe kwanaki da dama yana kammala shirin sauyin shekar, wanda ake hasashen zai bunkasa karfin ‘yan wasan tsakiyar United, tare da magance matsalolin tsaron baya dake damun kungiyar tsawon shekarar nan.