logo

HAUSA

Gwamnonin Najeriya sun yaba sosai kan hadin gwiwar kasarsu da kasar Sin

2024-09-05 13:27:16 CMG Hausa

A halin yanzu, ana gudanar da taron koli na Beijing na dandalin FOCAC, wato dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka na 2024 a Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda shugabanni da manyan jami'an gwamnatocin kasashen Afirka daban daban suka hallara, ciki har da na Najeriya, Nijar, Ghana da sauransu.

Yayin zantawa da wakilan sashen Hausa na CGTN a ran 4 ga watan Satumba, wasu gwamnonin jihohin Najeriya da suka zo kasar Sin don halartar taron, ciki har da na Kaduna da Neja, sun yaba sosai da hadin gwiwar Sin da Najeriya a fannonin tattalin arziki da kasuwanci.

Yayin zantawar, gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya bayyana cewa, hadin kai tsakanin jihar Kaduna da kamfanoni da lardunan kasar Sin ya kawo alheri da ci gaba ga jihar.

“Hadin kai da aka tattauna tsakanin shugabannin kasashen Sin da Najeriya wani abu ne wanda zai kawo ci gaba ga kasashen guda biyu. Amma a matsayina na gwamnan jihar Kaduna, na rattaba hannu da yarjejeniya da muka yi da kamfanin Huawei na kasar Sin, kuma zai kawo ci gaba a jihar Kaduna, abin da ya shafi fannin harkar tsaro, da harkar ilmi, da harkar kiwon lafiya, da harkar sufuri. Kuma watannin da suka wuce na je lardin Hebei, ni da kuma gwamnan Hebei din mun yi yarjejeniya mun saka hannu domin a je a gina wurin sana’o’i wanda za a yi a Kaduna, wanda har ma mun saka kamfanin Sin mai suna CCECC yanzu haka suna shirye-shirye za su fara wannan gini.”

A nasa bangaren, gwamnan jihar Neja, Umar Bag, ya yaba da gudunmawar da Sin ta bayar ga ci gaban zamani a bangaren aikin noma  a jiharsa.

“Mun kara dangon zumunci tsakanin kasar Sin da kasar Najeriya, bayan haka kuma, jihohi na Najeriya da jihohi na Sin sun hada dangantaka za su yi hulda a tsakaninsu ba tare da wani shamaki ba. Jihar Neja kasa ce ta manoma, muna da dimbin ruwa muna da dimbin fili, to wannan dama da muka samu, manoma da yawa na birnin Sin, sun nuna za su sa hannu a harkar noma, su taimaka mana da ilmin noma, da kuma abubuwan da zai taimakawa manomanmu, don su samu su yi noma mai kyau. ”