logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a kare tsarin kwance damarar makaman nukiliya da hana yaduwar makaman nukiliya

2024-09-05 13:58:19 CGTN Hausa

 

Ministan kasar Sin Sin na zaunanniyar tawagar Sin dake MDD Ren Hongyan ya yi jawabi a babban taron tunawa da ranar hana gwajin makaman nukiliya ta kasa da kasa da majalisar ta gudanar a jiya Laraba, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakan da suka dace don gaggauta aikin kwance damarar makaman nukiliya, da kuma kare tsarin kwance damarar makaman nukiliya da hana yaduwarsu bisa yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, ta yadda za a taka karin rawa don tabbatar da tsaron duniya ta bai daya.

Minista Ren ya ce, hana amfani da kuma murkushe makaman nukiliya daga tushe don tabbatar da babu irin makaman a duniya, ya dace da muradun Bil Adama na bai daya, kuma wannan shi ne matsayin da Sin ta dade take daukawa.

Minista Ren ya kuma jaddada cewa, lokacin da Sin ta mallaki makaman nukiliya, nan da nan ta yi alkwarin ba za ta yi amfani da su a duk wani yanayi ba tare da ko wani sharadi ba, musamman ma ga kasashen da ba su da makaman. Sin ta kayyade karfinta a wannan fanni dake iya kare tsaronta kawai, ba ta nufin yin takara da sauran kasashe a fannin karfin soja ba.

Kazalika, minista Ren ya ce, Sin tana rike da mukamin mai shiga tsakani na tsarin kasashe 5 dake mallakar makaman. Yana mai fatan wadannan kasashe za su tattauna kan matakan da za su dauka don rage hadarin makaman bisa tushen yarjejeniyar hana yaki da makaman da aka cimma a shekarar 2022. (Amina Xu)