WMO: PM2.5 ya yi kasa a kasar Sin da Turai a 2023
2024-09-05 10:19:45 CMG Hausa
Rahoton da hukumar kula da yanayi ta duniya ko WMO, ta wallafa a yau Alhamis ya nuna cewa, ma’aunin sinadarin PM2.5 mai gurbata iska na kasar Sin da Turai ya yi kasa da matsakaicin maki a shekarar 2023, sakamakon raguwar fitar hayaki mai gurbata iska.
Masanin kimiyya a hukumar ta WMO, Lorenzo Labrador ya ce, "Alkaluman 2023 sun nuna rashin daidaito, wanda ke nufin raguwar sinadarin PM2.5 din a kasar Sin da Turai idan aka kwatanta da lokaci tsakanin 2003 zuwa 2023.”
Kazalika, rahoton ya kuma ce munanan yanayi na sauyin yanayi, da gobarar daji da kuma gurbacewar iska na yin illa ga lafiyar dan adam, da muhalli da kuma aikin noma. (Yahaya)